Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na The National cewa, dubban mutanen turai sun gudanar da gagarumin jerin gwano da yin Allah wadai da kungiyar ‘yan ta’addan IS sakamakon ayyukan dambancin da kungiyar ke aikatawa kan bil adama a kasashen yankin gabas ta tsakiya da ma wasu kasashen.
A fili yake cewa kasashen Larabawa da na yammacin Turai su ne tushen samun tallafin kudade na kungiyoyin ta’addanci a duniya ciki har da kungiyar daular Musulunci a Iraki da Sham wato Da’ish. Sannan daga cikin kasashen Larabawan da suka fi shahara a fagen tallafawa ‘yan ta’addan kungiyar Da’ish da kudade da makamai su ne kasashen saudiyyaq qatar, Hadaddiyar Daular Larabawa da Jordan. Har ila yau akwai wasu hamshakan masu kudi daga kasashen Larabawa da suka yi fice a fagen tura daruruwan miliyoyin dalolin Amurka ga kungiyar Da’ish tare da gudanar da zaman tarurruka da manyan jami’an kungiyar domin karfafa ayyukan ta’addanci a kasashen Iraki, Siriya da kuma Lebanon.
Tuni dama tsohon fira ministan kasar Iraki Nuri Al-Maliki ya sha fitowa fili yana bayyana cewar kasashen Larabawa su ne kashin bayan karfafa ayyukan ta’addanci a yankin gabas ta tsakiya ta hanyar tallafawa kungiyoyin ‘yan ta’adda da makuden kudade ciki har da kungiyar Da’ish saboda cimma wasu munanan manufofinsu ta siyasa a yankin. Shi ma shugaban cibiyar bincike kan harkokin kasashen Larabawa a jami’ar Mainz ta kasar Jamus Professor Günter Mayer ya bayyana cewar kasashen Larabawa da suke yankin tekun Pasha musamman Saudiyya, Qatar, Kuwait da Hadaddiyar Daular Larabawa su ne kan gaba a fagen tallafawa kungiyar ta’addanci ta Da’ish da makuden kudade.
Mayer ya kara da cewar a halin yanzu da ta’addancin kungiyar Da’ish ya habaka kuma yake neman wuce makadi da rawa, sannan kungiyar ta samu damar zama da gindinta ta hanyar shelanta daular khilafa a kasashen Siriya da Iraki kuma take ci gaba da samun magoya baya daga sassa daban daban na duniya, hakan ya fara zama babban barazana ga gwamnatocin kasashen Larabawa.
1454725