Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Darul-Bar cewa, a jiya ne aka kammala gudanar da wata gasa harder kur'ani mai tsarki a kasar Saliyo wadda ta hada matasa da suka hardace kur'ani baki dayansa ko kuma wasu juzuoi.
Rahoton ya ci gaba da cewa wanann gasar ta kayar matuka, domin matasa 23 ne ad suka hardace kur'ani baki daya suka kasance daga cikin masu gudanar da gasar, gami da wasu matasan na daban da suka hardace wasu bangarori na kur'ani mai tsarki,a kan haka ne ma aka gudanar da gasar a matakai hudu, da suka hada da mataki na farko wato dukaknin kur'ani, da kuma sauran matakai na rabin kur'ani da kuma juzui goma da biyar.
Wadanda suka gudanar da bayanai a wurin sun ja hankulan matasa da su mayar da hankali wajen karatu da kuma harder kur'ani mai tsarki, kasantuwar hakan daya daga cikin ladubab da ya kamata musulmi ya kasance da su a cikin rayuwarsa, haka nan kuma an ja hankulan matasan da su riki koyarwar addinin muslunci a cikin dukaknin harkokin rayuwarsu, domin samun dacewa a rayuwa baki daya.