Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, a cikin wani bayani da ta fitar Hanan Ashrawi daya daga cikin manyan kusoshin kwaryakwaryan gwamnacin cin gishin kai ta palastinawa ta bayyana cewa shirin Isra’ila na bude kofar qatanin da ke cikin masallacin Qods yin hakan tamkar shelanta yaki ne kan dukkanin musulmi.
Wasu yahudawa masu tsattsauran ra'ayi sun yi cincirindo a yau a gaban babbar kofar masallacin Qods, domin tunawa da cika shekaru 46 da yahudawan sahyuniya suka mamaye birnin Qods da kuma kwace iko das hi daga hannun Palastinawa.
Shedun gani da ido sun tabbatar da cewa yahudawan masu tsattsauran ra'ayi sun afka a cikin harabar masallacin ne a yau Talata, kuma suna ta yi zantuttuka na batunci ga musulmi da addinin muslunci, daga cikinsu kuwa hard a wasu fitattun 'yan siyasa daga jam'iyyar Likud, inda suke cewa Qods ta yahudawa ce ba ta musulmi ko larabawa ba.
Kungiyoyin palastinawa 'yan gwagwarmaya bayan yin Allawadai da kakkausar murya kan wannan mummunan aiki, sun bayyana cewa wannan aiki ne na cin zarafin dukkanin al'ummar musulmin duniya, kuma hakan ya tabbatar wa duniya cewa haramtacciyar kasar Isra'ila ba a shirye take ta amince da hakkokin al'ummar palastinu ba.
1457773