IQNA

Koyar Da Darussan Akidar Muslunci A Jami'ar Musulunci Ta Kasar Ghana

21:23 - October 08, 2014
Lambar Labari: 1458529
Bangaren kasa da kasa, shugaban karamin ofishin jakadancin kasar Iran a kasar Ghana ya bayyana cewa ana shirin fara aiwatar da wani shiri na koyar da akidar muslunci a jami'ar kasar Ghana.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga bangaren yada labaransa na kasashen ketare cewa, Reza Bashayesh shugaban karamin ofishin jakadancin kasar Iran a kasar Ghana ya bayyana cewa ana shirin fara aiwatar da wani shiri na koyar da akidar muslunci a jami'ar da ke koyar da ilmomin addini.

Jami'in ya ce bangaren gudanarwa na jami'ar ne da kansa ya bukaci karamin ofishin jakadancin Iran day a dauki nauyin koyar da wadannan darussa da suka hada da akida, ilimin kalami, ilimin sanin makoma da kuma annabta da imanci, wanda kuma dukkanin darussa za su kasance da daraja hudu wadda jami'ar za ta lissafa ta  acikin sakamakon karatun dalibai.

Ya kara da cewa sun amince da wannan shiri, amma dai kuma za a gudanar das hi a wajen darussan da ake gudanarwa inda za a koyar da sua  lokacin da daliban ba su da wasu karatuka a jami'ar, kuma shirin zai fara ne daga gobe alhamis, kuma za a kammala a karshen watan bahman maizuwa.

1458114

Abubuwan Da Ya Shafa: ghana
captcha