IQNA

Tarjamar Kur'ani Mai Tsarki A Cikin Harshen Yau

20:30 - October 10, 2014
Lambar Labari: 1458732
Bangaren kasa da kasa, daya daga cikin shirin da ake fatan aiwatarwa a kasar Malawi a halin yanzu shi ne tarjamar kur'ani mai tsarki a cikin harshen yau daya daga cikin fitattun yarukan kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na ON Islam cewa, musulmin kasar Malawi na kokarin ganin sun gudanar da tarjamar kur'ani mai tsarki a cikin harshen yau daya daga cikin fitattun yarukan kasar da ke masu magana da shi.

Daya daga cikin mambobin majalisar malaman addinin muslunci a kasar ta Malawi Muhammad taha ya bayyana cewa, harshen Yau shi ne babban harshen da musulmin kasar suka fi yin amfani das hi, domin kuwa akasarin musulmin kasar sun fito ne daga wanan kabila, saboda haka maganar addinin muslunci a kasar Malawi ba tare da abaton waann harshe ba a kasar ba za a I babban tasiri ba, domin kuwa hatta malamai suna yin amfani da wannan harshe ne wajen yin wa'azi da fadakarwa a kasar.

A nasa bangaren babban sakataren majalisar malaman kasar Dr. Imran Sharif Muhammad, wanda ma babban malami ne da ake girmama shi a kasar ta Malawi, ya bayyana cewa tarjama kur'ani mai tsarki a cikin wannan harshe yana babban tasiri matuka wajen kara fito da ma'anonin kur'ani ga musulmi da kuma wadanda suke son fahimtar kur'ani da abin da ke cikinsa.

Kasar Malawi dai tana mutane kimanin miliyan 16, yayin da kashi kusan 36 cikin dari na mutanen kasar mabiya addinin muslunci ne, akasrin mutanen kuma mabiya addinin kirista ne.

1458654

Abubuwan Da Ya Shafa: malawi
captcha