IQNA

Yahudawan sahyuniya Sun kai Farmaki Kan Masallacin Aqsa

22:55 - October 16, 2014
Lambar Labari: 1460818
Bangaren kasa da kasa, yahudawan sahyuniya masu tsatsauran ra'ayi sun kaddamar da wani farmaki a yau a kan masallacin Qods mai alfarma tare da keta hurumin masallacin da kuma cin zarafin musulmi.


Kafanin dillancin labaran iqna ya habarat cewa, wasu gungun yahudawan sahyuniya masu tsatsauran ra'ayi sun kaddamar da wani farmaki a safiyar yau a kan masallacin Aqsa mai alfarma tare da keta hurumin masallacin da kuma abubuwa masu tsarki da ke wurin.

Rahotanni daga birnin Qods sun habarta cewa a yau wasu yahudawan sahyuniya masu tsattsauran ra'ayi sun kutsa a cikin a masallacin Qods mai alfarma. Rahotannin sun yi nuni da cewa sama da yahudawan sahyuniya 200 ne suka kutsa kai a cikin masallacin Qods mai alfarma a yau, inda suka yi ta rera taken tsokanar mabiya addinin musulunci da kuma mabiya addinin kiristanci, wadanda dukkaninsu suna girmama masallacin mai mai alfarma.

Kwamitin kare kare masallacin Qods wanda ya hada musulmi da kuma mabiya addinin kiristanci, ya kirayi musulmi da kiristoci da larabawa, da su safke nauyin da ya rataya kansu, wajen kare masallacin mai alfarma, da dukkanin wurare masu tsarki da ke gefensa, wadanda yahudawan sahyuniya suka sha alwashin kawar da su.

1460525

Abubuwan Da Ya Shafa: Qods
captcha