IQNA

Limamin Masallacin Qods Ya Bukaci "yanto Masallacin Daga Mamayar Yahudawa

22:20 - October 18, 2014
Lambar Labari: 1461400
Bangaren kasa da kasa, babban Alkalin birnin Qods mai alfarma ya yi kira ga gwamnatoci na kasasen musulmi da kuma na larabawa da su safke nauyin day a rataya akansu wajen yanto masallacin Aqsa mai alfarma daga sahyuniyawa.


Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin tashar talabijin ta palastinawa cewa Sheikh Taisir Al-Tamimi babban Alkalin birnin Qods ya yi kira ga gwamnatoci na kasasen musulmi da kuma na larabawa da su safke nauyin da ya rataya  a kansu wajen yanto masallacin Aqsa mai alfarma daga mamayar yahudawa sahyuniyawa na wannan zamani.

 

Sojojin Haramtacciyar Kasar Isra'ila sun kai farmaki a kan wasu palastinawa da suke gudanar da wani taro a cikin harabar masallacin Qods, domin girmama wasu kananan yara da suka samu nasara a gasar zanen masallacin mai alfarma.



Rahotanni daga birnin Qods sun habarta cewa tun kafin wannan lokacin an sanar da gudanar da taron, domin bayar da kyautuka ga wasu yara 'yan makaranta da suka shiga gasar zanen masallacin Qods, dakarun HKI sun kai farmaki a cikin harabar masallacin, inda suka kame wasu daga cikin wadanda suka shirya gudanar da taron, da kuma wani dan jarida, tare da firgita dukkanin kanan yara da suka hallara awurin.



A bangare guda wasu rahotannin sun yi nuni da cewa, a jiya sojin yahudawan sahyuniya sun harba wasu wasu makamai a kan sansanin palastinawa na Buraij, da ke tsakiyar yankin zirin Gaza, lamarin da ya yi sanadiyar yin shahadar wani matashi palastine dan shekara sha bakawai da haihuwa.



1461149

Abubuwan Da Ya Shafa: Qods
captcha