Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na World Bulletin cewa shugaban palastinawa Mahmud Abbas Abu Mazin ya bayyana cewa abin da haramtacciyar kasar Ira'ila take yin a tafka laifuka za ta gurfana a gaban kotu.
A nasa bangaren shugaban kwamitin kare masallacin qudus ya yi gargadi akan yadda ‘yan sahayoniya su ke yi wa alqiblar musulmi ta farko barazana. Shugaban Kwamitin kare masallacin na qudus, malam Ikramah sabri wanda ya yi hira da kafafen watsa labarun Palasdinu ya yi ishara da yadda ‘yan sahayoniyar su ke fakewaa da lokacin bukukuwansu na addini domin muzgunawa musulmi a cikin masallacin na qudus.
Malam sabri ya ci gaba da cewa; Takama da karfi da ‘yan sahayoniyar su ke yi da kuma muzgunawa palasdinawa ba zai taba basu nasarar shimfida ikonsu akan masallacin na qudus ba. A cikin kwanakin bayan nan dai ‘yan sahayoniyar suna tsananta kutsawa cikin masallacin na qudus da kuma takurawa musulmin da su ke salla a cikinsa. Da safiyar yau ne wasu yahudawa masu tsatsauran ra'ayi sun kwace iko da wasu gidajen palastinawa da ke yankin Salwan a gabacin birnin qods.
Wani jami'in cibiyar kula da lamurra Palastinawa mazauna gabacin birnin qods Jawad Siya ya sheda wa kamfanin dillancin labaran AFP cewa, yahudawan sun kwace manyan gine-gine guda biyu mallakain palastinawa a yau a gabacin birnin qods, bisa hujjar cewa sun sayi wadannan gine-gine da kowannensu ya kunshi gidage 10 a cikinsa, amma yahudawa ba gabatar da wata sheda ko dalili da ke tabbatar da abin da suke rayawa ba, kuma a lokacin da suke kwace iko da wadannan gine-gine 'yan sandan gwamnatin yahudawan Isr'aila ke rufa musu baya kuma suna ba su kariya.