Kungiyoyin kare hakkin bil adama da dama a kasashen duniya sun fara jan kunnen mahukuntan kasar Saudiyya dangane da hukuncin da wata kotun kasar ta yanke a kan daya daga cikin manyan malaman mazhabar shi'a a kasar, Sheikh Namir Muhammad Baqir Namir.
Kotun kasar ta Saudiyya dai ta yanke hukuncin kisa ne a jiya Laraba a kan Sheikh Namir, bisa tuhumarsa da sukar salon mulkin mulukiya na masarautar Al-saud a kasar ta Saudiyya a cikin hudubobin sallar Juma'a da yake gabatarwa a masallacinsa da ke yankin Awamiyya a cikin gundumar Qatif da ke gabacin kasar.
Gamayyar wasu kungiyoyin kare hakkin bil adama a kasar Birtaniya da ma wasu kasashen turai da na larabawa, sun gargadi mahukuntan kasar ta Saudiyya da su shiga taitayinsu a kan hankoronsu na ganin sun kashe Sheikh Namir, wanda a cewar kungiyoyin aiwatar da wannan hukunci na siyasa zai jefa kasar cikin wani mawuyacin hali, wanda masarautar kasar ce za ta dauki alhakin hakan.
Sheikh Namir dan shekaru 55 da haihuwa ya sahara a kasar Saudiyya da ma kasashen larabawa, wajen gwagwarmayarsa ta kare hakkokin mutane da ake zalunta, da kuma bude cibiyoyin ilimi da wayar da kan al'umma kan harkoki na zamantakewa da kuma siyasa a addinance, wannan ya sanya shi ya samu karbuwa a wajen mutane da dama a kasar ta Saudiyya, mabiya mazhabar shi'a da ma wadanda ba su ba, musamman talakawa daga cikin mutanen kasar, sakamakon tunkarar sarakunan kasar da yake yi tare da fada musu gaskiya, abin da sauran malaman kasar ba za su iya yi ba.
A cikin watan Agustan 2008 gwamnatin Saudiyya ta kafa masa takunkumin na hana shi gabatar da laccoci ko fitar da makaloli da sauran rubuce-rubuce da ya saba yi, na addini ne ko na siyasa ko kuma na zamantakewa, tare da sanya idon jami'an tsaro a kansa.
A cikin watan Oktoban shekara ta 2011 al'ummomi a yankunan Qatif da Ihsa da kuma Awamiyyah da ma sauran yankunan gabacin Saudiyya wanda akasarin mazauna wadannan yankuna mabiya mazhabar shi'a ne, kuma a nan ne dukkanin arzikin danyen manfetur da iskar gas da kasar Saudiyya take da shi yake, suka fito suna nuna rashin amincewarsu da salon mulkin mulukiya na kasar, tare da neman a saki dubban fursunonin siyasa da mahukuntan kasar suke tsare da su, tare da neman a yi adalci wajen rabon arzikin kasar musamamn ma ganin cewa arzikin manfetur da iskar gas da kasar Saudiyya ta dogara da shi daga yankinsu ake fitar da shi, amma mahukuntan kasar sun yi amfani da karfi wajen murkushe su tare da kashe adadi mai yawa da kuma kame wasu dubbai daga cikinsu, wanda hakan ya sanya Sheikh Namir ya fito ya soki wannan mataki da mahukuntan kasar suke dauka kan fararen hula masu zanga-zangar lumana domin neman hakkokinsu da aka haramta musu.
A ranar 8 ga watan Yulin 2012 mahukuntan Saudiyya sun tura jami'an tsaro a cikin shirin yaki zuwa gidan Sheikh Namir a garin Awamiyya, inda suka yi harbe-harbe a kan gidan nasa tare da firgita iyalansa, yayin da shi kuma suka harbe shi da harsasan biga 4 a kafarsa, daga nan suka tafi da shi kurkuku, inda a jiya Laraba kotu ta yanke masa hukuncin kisa, bisa tuhumarsa da goyon bayan masu zanga-zangar kin jinin masarautar kasar da kuma sukar salon siyasa da mulkin wannan masarauta.
1462057