IQNA

An Gudanar Da Gasar Hardar Kur'ani Mai Tsarki Ta Daliban Sakandare A Ethiopia

20:17 - October 22, 2014
Lambar Labari: 1463057
Bangaren kasa da kasa an gudanar da gasar hardar kur'ani mai tsarki wadda ta kunshi daliban makarantun sakandare musulmi a bangaren hardar kur'ani mai tsarki a kasar Ethiopia.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na hqmi.org cewa, a jiya ne aka fara gudanar da gasar hardrr kur'ani mai tsarki a garin Harar na kasar Habasha wadda ta kunshi daliban makarantun sakandare musulmi a bangaren harder kur'ani mai tsarki.
Wannan gasa dai an shirya ta ne da nufin karfafa dalibai musulmi da suke da shawa'ar fada ayyukansu na kur'ani, musamman a bangaren karatu da kuma harda, wanda hakan yana daga cikin ayyukan da babban kwamitin kula da ayyukan kur'ani na majalisar musulmin kasar yake daukar nauyin shirya da kuma gudanarwa lokaci zuwa lokaci.
Kasar Habasha dai ta kasance daya daga cikin kasashen masu tsohon tarihi da ke nahiyar Afirka, inda ta taka rawa a bangarori da daman a ci gaban dan adam da kuma dadaddiyar sira gami da al'adu, haka nan kuma sun bayar da gudunmawarsu ga musulmi a lokacin da suka hijira zuwa kasar a farkon bayyanar addinin musluci, kasantuwarsu mabiya ne ga addinin kiristanci, kuma har yanzu akasarin mutanen kasar suna kan wannan turba, duk kuwa da cewa addinin muslunci shi ne na biyua  kasar.
1462323

Abubuwan Da Ya Shafa: habasha
captcha