IQNA

Ta'addancin Ayyukan Takfiriyyah Su Ne Mafi A Tsawon Tarihi

20:40 - October 28, 2014
Lambar Labari: 1465131
Bangaren kasa da kasa, babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon Sayyid Hasan Nasrallah ya bayyana abin da kungiyoyin takfiriya masu kafirta musulmi suke yi a halin yanzu a matsayin mafi munin bata sunan Musulunci da aka taba yi tsawon tarihi.

Kamfanin dillancin labaran kur'ani na Iqna ya habarta cewa, Sayyid Hasan Nasrallah ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da jawabin juyayin Ashura a daren jiya Litinin a birnin Beirut, babban birnin kasar Labanon inda ya ce ko shakka babu dabi’u da halayen masu kafirta musulmin yana nesanta wadanda ba musulmi ba daga Musulunci yana mai cewa: “Masu kafirta musulmin suna kisa da yanka mutane suna masu kafa hujja da kare wannan danyen aiki na su da ayoyin Alkur’ani da hadisan karya da aka jingina su ga Ma’aikin Allah (s.a.w.a).
Sayyid Nasrallah ya ce ko shakka babu abin da ke faru a halin yanzu a kasashen musulmi, babbar barazana ce ga Musulunci da kuma al’ummar musulmi, da ke bukatar malaman Musulunci,’ yan Shi’ansu da ‘yan Sunnarsu, su tsaya kyam wajen fada da shi da kuma bayyanar wa da duniya Musulunci na hakika.
Daga karshe sai shugaban kungiyar ta Hizbullah ya kirayi kasar Saudiyya da cewa ita ce take da alhakin farko na dakatar da yaduwar wannan akida ta kafirta musulmi don kuwa ita ce ta gina da kuma daukan nauyin irin makarantun da suke yaye dalibai masu wannan akida ta kafirta musulmi.

1464693

Abubuwan Da Ya Shafa: sayyid
captcha