IQNA

Firayi ministan Palastinu Ya Ziyarci Masalalcin Qods Mai Alfarma

23:48 - October 29, 2014
Lambar Labari: 1465585
Bangaren kasa da kasa, firayi ministan palastinu ya yi wani rangadi a birnin Qods inda ya ziyarci masallacin Aqsa mai alfarama domin ganewa idanunsa halin da ake ciki a yankn.

Kamfanin dillancin labaranIqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na World Bulletin cewa, Hamdsallah firayi ministan palastinu ya yi wani rangadi a birnin Qods inda ya ziyarci masallacin Aqsa mai alfarama domin ganewa idanunsa irin baranar da yahudawa suke tafkawa.
Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila na shirin gina wasu matsugunnan yahudawa ‘yan share wuri zauna a cikin yankunan palastinawa da suka mamaye a gabacin birnin Qods. Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin cikin gida ta haramtacciyar kasar Isra’ila Ifrat Aubrah ta bayyana cewa, ma’aikatar harkokin cikin gidan ta amince da batun gina wasu sabbin matsugunnan yahudawa kimanin 1500 zuwa 1600 a cikin yankunan gabacin birnin Qods, kuma da zaran an kammala dukkanin abin ya kamata za a fara aiwatar da wannan shiri.
Anasa bangaren kakakin hukumar kwarkwaryancin cin gishin kai ta palastinawa abu rudainah ya bayyana cewa, suna yin Allawadai da wannan mataki, kuma idan haramtacciyar kasar ba ta dakatar da wannan shiri ba, za su mika batun ga kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya.
1464986

Abubuwan Da Ya Shafa: Qods
captcha