IQNA

Yan Si’a Na Masar Sun gayyaci Malaman Azhar Zuwa Taron Ashura

0:01 - October 30, 2014
Lambar Labari: 1465586
Bangaren kasa da kasa, rahotanni daga masar sun ce mabya mazhabar shi’a a Masar sun gayyaci malaman jami’ar muslunci ta Azhar zuwa tarukan Ashura na Imam Hussain (AS) a kasar.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daha shafin sadarwa na bawaba cewa, ‘yan shia mabya mazhabar shi’a a Masar sun gayyaci malaman jami’ar muslunci ta Azhar zuwa tarukan Ashura na Imam Hussain (AS) a kasar domin tunawa da abin da ya samu Ahlul bait (AS) a wannan rana.
A can manama kuwa an nakalto nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo alwasat cewa jami’an masarautar kasar da ke tsananin adawa da mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah na kasar sun rusa wani alamin Ashura Imam Hussain (AS) da aka kafa a shirin fara juyin da ake yi nan ba da jimawa ba kamar dai yadda aka saba yin haka daruruwan shekaru da suka gabata a kasar.
Wasu rahotannin kuma sun wata kotu a kasar ta yanke hukuncin dauri a gidan kurkuku kan wasu fararen hula ashrin sakamakon fafatukar da suke yi na neman gudanar da gyara a harkar siyasar kasar.
Kamfanin dillancin labaran faransa ya bada labarin cewa; Wata kotu a kasar a yau Laraba ta yanke hukuncin daurin shekaru goma kan mutane ashirin da shida yayin da ta daure wasu mutane uku na daban shekaru uku a gidan kurkuku kan zargin hannu a kai hari kan wani ofishin ‘yan sanda a kasar.
Mutanen ashirin da tara sun yi watsi da zargin da jami’an ‘yan sanda ke yi kansu a gaban kotun, amma kotun ta ki saurarensu saboda rahoton da rundunar ‘yan sandan kasar ta gabatar kan su tare da shaidar furucin da ta tatsa daga gare su ta hanyar tursasawa a lokacin da suke tsare a wajen ‘yan sanda.
1465418

Abubuwan Da Ya Shafa: masar
captcha