Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Masdark cewa, a jiya an nuna wani dadadden kwafin kur'ani mai tsarki mallakin masallacin Qods mai alfarma wanda tarihinsa ke komawa zuwa ga shekaru da dama da suka gaba wanda kai tsawon karni uku kamar dai yadda majiyoyin angaren kula da masallacin suka tabbatar.
Wasu bayanan kuma na daban na cewa jami'an tsaron haramtacciyar kasar Isra'ila na ci gaba da yin dauki ba dadi da matasan palastinawa a yankunan da ke gabacin birnin na Qods.
Yan sandan haramtacciyar kasar Isra'ila sun kai samame a gidan mahaifan matasin nan Abdulrahamn Shaludi, wanda ya banke wasu yahudawa a birnin Qods da mota, inda ya kashe daya kuma ya jikkata wasu 8, kafin jami'an 'yan sanda su harbe shi, 'yan sandan na Isra'ila sun kame dan uwansa shakiki Izzuddin Shaludi da kuma wasu mutane 5 a cikin danginsa.
Ya kara da cewa matasan apalastinawa suna ci gaba da yin dauki ba dadi tsakaninsu da jami'an tsaron yahudawan, wadanda ke amfani da harsasan roba da kuma masu rai gami da barkonon tsohuwa domin tarwata matasan masu bore, amma duk da haka har zuwa tsakar daren jiya ana bata kashi tsakanin bangarorin biyu a unguwannin da ke gabacin birnin Qods.
1465378