IQNA

Kwararan Matakan Tsaro Domin kare Rayukan Masu Tarukan Ashura A Karbala

18:15 - November 02, 2014
Lambar Labari: 1466858
Bangaren kasa da kasa, jami’an tsaron Iraki sun sanarcewa an fara gudanar da matakan tsaron da suka tsara don ba da kariya ga miliyoyin musulmin da za su tafi garin Karbala daga kasashen duniya daban-daban domin raya bukukuwan Ashura na Imam Hussain (AS) a karbala.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ma’aikatar tsaro da ta cikin gida ta kasar Iraki sun sanar da fara gudanar da matakan tsaron da suka tsara don ba da kariya ga miliyoyin musulmin da za su tafi garin Karbala don raya bukukuwan Ashura da za a fara gudanarwa a yau din nan juma’a.
A yayin da ya ke sanar da hakan, kakakin ma’aikatar tsaron kasar Irakin Kanar Dhiyah Al-Wakil ya ce tuni jami’an tsaron kasar da suka fito daga cibiyoyi daban-daban na tsaron suka fara gudanar da ayyukansu don tabbatar da tsaro da kuma kiyaye lafiyar masu ziyarar Karbala a hanya da kuma a cikin garin.
Shi ma a nasa bangaren kwamandan dakarun tabbatar da tsaron Karbalan Usman Ganmani ya ce sun tanadi kimanin jami’an tsaro dubu talatin don tabbatar da tsaron masu ziyarar.
Tun dai bayan kifar da gwamnatin kama-karya ta Saddam Husaini a kasar, miliyoyin musulmi ne suke tafiya garin na Karbala don raya bukukuwa Ashura don tunawa da irin kisan gillan da aka yi wa Imam Husaini (a.s) da sauran iyalai da sahabbansa a Karbala din a shekara ta 61 bayan hijira Ma’aiki (s.a.w.a). A kowace shekara kuma gwamnatin Iraki ta kan dauki matakan tsaro don hana ‘yan ta’addan da suke kai wa irin wadannan tarurrukan hari cimma bakar aniyarsu.
1466597

Abubuwan Da Ya Shafa: ashura
captcha