IQNA

An Gudanar Da Tarukan Daren Tasu'a Tare Da Halartar Jagoran Juyin Islama

19:06 - November 03, 2014
Lambar Labari: 1469964
Bangaren siyasa, an gudanar da zaman juyayi na daren Tasu'a a Huainiyar Imam khomeni (RA) tare da halartar jagoran juyin juya halin muslunci a Iran Ayatolla Sayyid Ali Khamenei.

Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya nakalto daga shafin jagora cewa, an gudanar da taron juyayin shahadar shugaban shahidai Imam Husain (a.s) da mabiyansa na farko a wannan shekarar a Husainiyar Imam Khumaini (r.a) da ke gidan Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei.
Hujjatul Islam wal muslimin Sheikh Kazim Siddiqi ne ya gabatar da jawabi a wajen wannan taron wanda ya sami halartar Jagoran juyin juya halin Musuluncin bugu da kari kan wasu daga cikin manyan jami'an Jamhuriyar Musulunci ta Iran da dubun dubatan al'ummar kasar. A jawabin nasa, Sheikh Kazim Siddiqi ya karin haske kan manufar yunkuri da mikewar da Imam Husaini (a.s) ya yi inda ya ce: Kyautata lamurra, umurni da kyawawan ayyuka da hani da munana, tsayar da hakki da kwance wa azzalumai da mabarnata zani a kasuwa, wasu ne daga cikin manufofin wannan yunkuri na Imam Husai (a.s). Kuma lalle ya cimma wadannan manufofi na sa sannan kuma yayi nasara.
Haka nan kuma yayin da ya ke bayanin cewa Allah Madaukakin Sarki ba zai taba barin kafirai su yi galaba a kan musulmi ba, Hujjatul Islam Kazim Siddiqi cewa ya yi: Ma'abota 'yanci na duniya sun kasance ne a sansanin jihadi da tsayin daka na Imam Husaini, amincin Allah ya tabbata a gare shi, inda suka yi tsayin daka da kuma tinkarar ma'abota girman kai da 'yan mulkin mallaka. Ta haka ne suka kawar wa azzaluman masu mulki tsaro da zaman lafiya.
Hujjatul Islam Siddiqi ya kara da cewa: Juyin juya halin Musulunci na Iran ma ya samo asali ne daga wannan yunkuri na Imam Husaini. Hakan ne ya sanya a yau ba za mu iya yin watsi da mutumcinmu don samun wani abu na daban ba.
Har ila yau a yayin wannan taron Malamai Bani Fatimi da Mahdi Salahshur sun gabatar da wakoki da bayanan abubuwan da suka faru ga Imam Husaini (a.s) da mabiyansa a Karbala.
1466866

Abubuwan Da Ya Shafa: ashura
captcha