IQNA

19:13 - November 03, 2014
Lambar Labari: 1469966
Bangaren kasa da kasa, ana yada batun yin afuwa ga babban malamin addinin muslunci kuma jagoran mabiya mazhabar shi'a a Saudiyya wanda mahukuntan kasar suka yanke wa hukuncin kisa a kwanakin baya saboda dalilai na siyasa.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na cibiyar mazhabar ahlul bait ta duniya cewa, ana ta batun yin afuwa ga babban malamin addinin muslunci kuma jagoran mabiya mazhabar shi'a a Saudiyya da aka yanke wa hukuncin kisa a kwanakin baya saboda dalilai na siyasa a kasar, tun bayan da Ayatollah Hashemi Rafsanjani ya aikewa sarkin Saudiyya Abdullah Bin Abdulaziz da wasika, amma babu wata majiya ta Saudiyya da ta tabbatar da hakan.

A nasu bangaren iyalan babban malamin Shi’an na kasar Saudiyya Ayatullah Nimr Baqir al-Nimr sun musanta labarin da wasu kafafen watsa labarai suke wata na cewa gwamnatin ta Saudiyya ta yi masa afuwa.
Shafin watsa labaran kasar Labanon ya jiyo daya daga cikin iyalan Shiek al-Nimr din wanda bai so a bayyana sunansa yana fadin cewa babu inganci cikin labaran da wasu kafafen watsa labarai suke watsa na yin afuwa ga Shiek al-Nimr din.
Har ila yau iyalan Sheikh al-Nimr din sun ce nan da ‘yan kwanaki masu zuwa, kafin cika kwanaki talatin din da doka ta tanadar, zai daukaka kara kan hukuncin kisan da aka yanke don bukatar da a yi watsi da shi.
Iyalan Shehin malamin dai suna ganin akwai wani makirci cikin yada irin wadannan labarai marasa tushe dangane da wannan hukunci da aka yanke masa wanda har ya zuwa yanzu ake ta Allah wadai da shi a bangarori daban-daban na duniya.
1466608

Abubuwan Da Ya Shafa: Saudiyyah
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: