IQNA

Tashar Talabijin Ta Almayadeen Tashe Ce Da Ke Kare Manufar Gwagwarmaya

16:12 - November 12, 2014
Lambar Labari: 1472736
Bangaren kasa da kasa, tashar talabijin ta Almayadeen tana taka gagarumar rawa wajen yada manufofi na gwagwarmaya da zaluncin yahudawa a kan al’ummar musulmi da larabawa da kuma yadda za a tunkari wannan lamari.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wata zantawa da ta hada shi da shugaban tashar talabijin ta Almayadeen Gassan Bin Judduh ya bayyana cewa wannan tasha ta Almayadeen tana taka gagarumar rawa wajen yada manufofi na gwagwarmaya da zaluncin yahudawa a kan al’ummar musulmi da larabawa tare da wayar da kan al’umma dangane da yadda za a tunkari wannan lamari a cikin kasashen musulmi da na larabawa.
Ya ci gaba da cewa bisa la’akari da cewa wannan tashar ba ta jima da fara ayyukanta ba, amma kuma  acikin kankanin lokaci ta samu karbuwa matuka a tsakanin al’ummomin musulmi da na larabawa, bugu da kari hakan wasu daga cikin al’ummomin wasu daga cikin al’ummomin wasu kasashe da suke kiyayya da zaluncin turawa suna nuna gamsuwa da yadda wannan tashe take gudanar da ayyukanta, daga ciki kuwa har da mutanen latin.
Daga cikin muhimman ayyukan da tashar talabijin ta Almayadeen take gudamnarwa akwai shirin labarai da kuma zantawa da masana daga dukkanin bangarori na duniya, haka nan kuma tana gabatar da shirye-shirye na addini wanda kan mayar da hankali kan abubuwan ad suke faruwa  acikin duniya musulmi, da kuma yadda ya kamata a tunkari lamurran inda akan gayyaci malamn addini da kuma masana.
1472197

Abubuwan Da Ya Shafa: almayadeen
captcha