IQNA

Kungiyar Kasashen Musulmi Za Ta Fara Zamanta kan batun Qods

16:48 - November 15, 2014
Lambar Labari: 1473480
Bangaren kasa da kasa, kungiyar kasashen musulmi na shirin gudanar da zamanta dangane da batun Qods da kuma ta’addancin yahudawan sahyuniya a kansa da kuma al’ummar palastinu.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Anadolu Agency cewa, a cikin wannan mako kungiyar kasashen musulmi na shirin gudanar da zamanta dangane da batun Qods da kuma ta’addancin yahudawan sahyuniya a kansa.
A wani labarin kuma wata kotu ta musamman da ke bin kadun hakkokin bil adama da aka kafa kan keta hurumin dan adam da yahudawan sahyuniya ke yi a yankin Palastine, mai suna The Russell Tribunal on Palestine, ta kirayi kotun manyan laifuka ta duniya da ke birnin Hague na kasar Holland, ta gudanar da bincike kan muggan laifukan da haramtacciyar kasar Isra'ila take aikatawa kan Palastinawa.  
Kotun ta yi wannan kira ne a zaman da ta gudanar a birnin Brussel na kasar Belgium wanda aka kammala jiya Lahadi, inda ta yi bitar rahotanni da bayanai da ta harhada daga wakilanta masu sanya ido a Palastinu, da kuma kungiyoyin kare hakkin bil adama na kasa da kasa, kan yadda haramtacciyar kasar Isra'la take cin zarafin Palastinawa da kuma aikata laifukan yaki a kansu, inda ta bukaci kotun manyan laifuka ta duniya da ta kafa wani kwamiti mai zaman kansa karkashin kulawar majalisar dinkin duniya, domin ya gudanar da bincike kan wadannan laifuka.  
An kafa wannan kotu ne dai tun a cikin watan Maris din shekara ta 2009, da nufin bin kadun laifukan da haramtacciyar kasar Isra'ila take aikatawa kan Palastiniwa, sakamakon yin watsi da nuna halin ko in kula da akasarin kasashen duniya suke yi da wannan batu, musamman kasashen yammacin turai da ke da'awar kare hakkin bil adama. Kotun dai bangare ce na kungiyar kare hakkin bil adama da masanin ilimin falsafa na kasar Birtaniya Bertrand Russel ya kafa, wadda a halin yanzu take da mambobi daga kasashen duniya daban-daban, da suka hada da manyna lauyoyi da masana kan harkokin shari'a.
1472920

Abubuwan Da Ya Shafa: Qods
captcha