Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na na Al-ahad cewa, Aytaollah Ozma Bashir Najafi daya daga cikin manyan malaman addinin muslunci a kasar Iraki ya bayyana addinin muslunci da cewa shi ne zaman lafiya da rangwane da kaunar juna da kuma kyawawan dabiu kuma shi ne abin da yake koyar dad an adam.
Shehin malamin ya bayyana hakan ne yau a lokacin da ya kai wata ziyara a kudancin kasar Lebanon, inda ya samu tarba daga manyan malaman addini na yankin, da suka hada da sheikh Abdul amir Qabalan da Sheikh Muhammad Juma'a wakilin kungiyar Hizbullah a yanki da dai sauran malamai da manyan mutane, wadanda suka yaba da irin matakan da yake dauka wajen wayar da kan al'ummar musulmi tare da bayyana musu hakikanin addini da kuma koyarwarsa.
Ayatollah Bashir Najafi ya bayyana irin muhimmancin da ke tatatre da yin aiki da koyarwar addinin muslunci ta hakika, domin kuwa ita ce abin da dan adam ke bukata a cikin bangarori na rayuwarsa, kuma musulmi ne za su bayyana wa sauran al'ummomi wannan koyarwa ta hanyar ayyukansu da kuma yin riko da ita, ta yadda ayyukan musulmi na kwarai za su zama su ne sune suke bayyana hakikanin koyarwar addininsu.