Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na SANA cewa, a jiya cinciridon musulmi ne suka gudanar da jerin gwano a gaban ofishin jakadancin kasar Saudiyya a birnin Kanbara na kasar Australia domin neman a saki Ayatollah Nimir da mahukunatn Saudiyya ke ci gaba da tsare shi saboda ra’ayoyinsa na kiyaya da zalunci.
A nasu bangaren kungiyoyin kare hakkin bil adama da dama a kasashen duniya sun fara jan kunnen mahukuntan kasar Saudiyya dangane da hukuncin da wata kotun kasar ta yanke a kan daya daga cikin manyan malaman mazhabar shi'a a kasar Sheikh Namir Muhammad Baqir Namir a cikin yan kwanakin nan.
Wata kotun kasar ta Saudiyya dai ta yanke hukuncin kisa ne a jiya Laraba a kan Sheikh Namir, bisa tuhumarsa da sukar salon mulkin mulukiya na masarautar Al-saud a kasar ta Saudiyya a cikin hudubobin sallar Juma'a da yake gabatarwa a masallacinsa da ke yankin Awamiyya a cikin gundumar qatif da ke gabacin kasar ta Saudiyya.
Haka nan kuma gamayyar wasu kungiyoyin kare hakkin bil adama a kasar birtaniya da ma wasu kasashen turai da na larabawa, sun gargadi mahukuntan kasar ta Saudiyya da su shiga taitayinsu a kan hankoronsu na ganin sun kashe Sheikh Namir, wanda a cewar kungiyoyin aiwatar da wannan hukunci na siyasa zai jefa kasar cikin wani mawuyacin hali.
1474488