Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya habarta cewa a ci gaba da gudanar da zaman taron malamai da ake gudanarwa a birnin Qom na jamhuriyar muslunci ta Iran daya daga cikin fitattun malaman addinin muslunci daga Masar da ya halarci zaman taron Tajuddin Hilali ya bayyana cewa dole ne malamai su hada kai domin tunkarar akidar kafirta musulmi.
An bude taron kasa da kasa kan hadarin masu masu akidar kafirta Mutane a birnin Qom dake nan Jamhuriyar Musulunci ta Iran An buda taron ne da jawabin babban malamin nan Ayyatullahi Nasir makarimu Shirazi, kuma wannan taro zai dauki wini biyu ana gudanar da shi.
Manufar wannan taro dai bayyana duniya manufar masu akidar kafirta mutane a ilmance , inda suka fito, kisan musulimi da sunan musulnci, batawa Addinin Islama kuma taron zai tattauna kan hanyoyin da ya kamata Al’ummar musulmi ta dauka domin tsarkake kanta daga wannan bala’i.
A cewar Hujatul Islam Sayyid Mahdi Ali Zade Musawi, sakatare tsare wannan taro, kimanin Masana 318 ne ke halartar wannan taro wadanda suka fito daga kasashe 83 na duniya. Kuma an gabatar da wannan littafi mai shafi dari bakawai wanda ya hada makalar wadanan malimai kan hadarin masu akidar kafirta mutane da sunan musulinci.
1476458