IQNA

Sami Yusuf Na Kokarin Fito Kyakkyawar Fuskar Musulmi A Yammacin Turai

17:56 - February 19, 2009
Lambar Labari: 1746085
Bangaren kasa da kasa: Shahararren mawakin nan musulmi (Sami Yusuf) dan kasar Birtaniya, na kokarin fito kyakkyawar fuskar addinin muslunci ta hanyar shirya wata waka ta musamman kan hakan.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na ( Al-bashair)cewa; a wata gtattaunawa da ta hada shi da kamfanin dillancin labarai na Reuters, Sami Yusuf ya bayyana cewa ya shirya wakar ne domin ya nuna wa al'ummomin kasashen yammacin turai da ma na duniya baki daya cewa; addinin musulunci addini ne na zaman lafiya da fahimtar juna tsakaninsa da sauran addinai da al'adu, kuma kokarin da wasu ken a bayyana addinin musulunci da cewa addini ne na t'addanci, hakan kuskure ne. Ya kara da cewa yana bin koyarwa ta sahihin addinin musulunci ne, ba musuluncin Bin Laden ba.

365778


captcha