Bangaren kasa da kasa: Wani fitaccen malamin addinin musulunci a kasar Saudiyya Abdulmohsen Al-abikan, ya yi kakkausar kan yadda ake rushe muhimman wuraren tarihin addinin musulunci a kasar da sunan kawar da shirka.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; Sheikh Abdulmohsen Al-abikan ya yi kirayi mahukuntan kasar Saudiyya da su dauki matakan kare muhimman wuraren tarihi na addinin musulunci da ke kasar da sunan yunkurin kawar da shirka, ya ce babu wani dalili da zai sanya a rushe wurare masu tsarki a tarihin musulunci da sunan ana koakrin hana shirka ne tsakanin musulmi. Bayanai masu tushe sun tabbatar da cewa wasu masu tsattsauran ra'ayin wahabiyanci a kasar sun rushed a dama daga cikin wurare masu tsaki da sunan hana shirka.
366746