Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar (Al-sharq) ta kasar Qatar cewa; kur'anin da aka rubuta a kasar Qatar, an mika shi ga manyan malaman addini na jami'ar Al-azhar domin duba shi, da kuma duba salon da aka yi amfani da shi wajen rubutun, kuma dukkanin malaman sun gamsu da yadda aka rubuta kur'anin, wanda aka kira da sunan Mushaf Qatar, kuma tuni jami'ar Al-azhar ta bayar da izini ga kwamitin da ke gudanar ayyuka da suka shafi rubutawa da kuma buga wannan kur'ani, da a buga kur'anin ba tare da wata matsala ba.
Kur'anin dai yana da wani nau'in rubutu, wanda shi ne irinsa na farko da za a buga, kamar yadda ya sha banban ta fuskacin shafukansa.
368936