IQNA

3- Muftin Kasar Labanon Ya Yi Allah Wadai Da Cin Mutuncin Annabawa (AS) Da Yahudawa Ke Yi

Bangaren Siyasa Da zamantakewa: Makki Muftin kasar labanon a a wani taron yan shia a wannan kasa ya fitar da wani bayani da a ciki yake Allah wadai da cin mutuncin da Gidan talbijin din HKI ke Yiwa Annabi Isa (AS) da ma'aifiyarsa Maryam (AS) Da kuma Ma'aikin Allah Annabi Muhammadu (SWA).
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ce daga Labanon ta watsa rahoton cewa: Makki bayan ya yi Allah wadai da wannan mataki na gwamnatin Haramtacciyar kasar isra'ila ya kuma yi Allah wadai da yadda wata jarida ta cikin gida a Haramtacciyar kasar Isra'ila ke batamci a tarihin Imam Huseini (AS) a wani mataki na takwalar fada da neman haddasa rikici .Ya kara da cewa: Tarihin Imam Husein (AS) yana daya daga cikin tarihi masu inganci na hankali don haka duk wanda zai kawo shaku a cikinsa da yin maganganun batanci ba za amince da hakan ba.

373579