IQNA

Ranar 'Yan Jarida Ta Duniya Rana Ce Bayyana 'Yanci Da Hakikanin Musulunci

17:55 - May 04, 2009
Lambar Labari: 1773958
Bangaren kasa da kasa; Ranar 'yan jarida ta duniya rana ce ta bayyana hakikanin koyarwa irin ta addinin Musulunci, ta fuskacin fadada fahimta tsakanin yaruka da al'adu da kuma tattaunawa tsakanin addinai da taimaka wa yunkurin tabbatar da sulhu da tsaro a fadin duniya.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC cewa; shugaban kungiyar Akmaluddini ihsan ya bayyana cewa; Ranar 'yan jarida ta duniya rana ce ta bayyana hakikanin koyarwa irin ta addinin Musulunci, ta fuskacin fadada fahimta tsakanin yaruka da al'adu da kuma tattaunawa tsakanin addinai da taimaka wa yunkurin tabbatar da sulhu da tsaro a fadin duniya. Ya ci gaba da cewa bisa la'akari da taken da aka baiwa wannan wannan shekara ta 'yan jarida shi ne; rawar da kafofin yada labarai za su taka wajen kara farfado da tattaunawa tsakanin addinai da kuma samun sulhu da zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin al'ummomin dsuniya, ya ce wannan dam ace ta bayyana hakikanin addinin Musulunci.

398618





captcha