IQNA

Bangaren fasaha da al'ada: ministan sadarwa na kasar Afganistan ne ya bada labarin fara tace shafofin Internet da ke cin mutuncin addinin musulunci da kuma sabawa kyawawan dabi'u a wannan kasa.
Daga Afganistan ne cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ce ta watsa rahoton cewa: Amirzi Sangin ministan sadarwa na kasar Afganistan bayan ya bayyana bakin ciki da bacin rai kan yadda wasu ke amfani da shafofin Internet wajen cin zarafin addinin musulunci da kuma yada mummmunan halaye da cewa; yanzu sun kawo wasu na'urori da za su rika tace irin wadannan shafofi na internet da kuma dakile mummunar manufar makiya addinin musulunci.


407776