IQNA

15:52 - May 27, 2009
Lambar Labari: 1783987
Bangaren kasa da kasa: Daraktan jami'ar musulunci da ke birnin Riyad na kasar saudiyya Sulaiman Aba khalil ya bayyana cewa, za a bude wata cibiya ta yin nazari kan harkokin banki a musulunce a cikin wannan jami'a.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar shark alausat cewa; a wata zantawa da ta hada jaridar da kuma daraktan jami'ar musulunci da ke birnin Riyad na kasar saudiyya Sulaiman Aba khalil ya bayyana cewa, za a bude wata cibiya ta yin nazari kan harkokin banki a musulunce a cikin wannan jami'a. Ya ci gaba da cewa masana kan harkokin tattalin arziki da harkokin banki za su bayar da gudunmawarsu wajen hada bayanai da cibiyar ke bukata domin masu nazari kan harkokin banki da kudi a musulunce, da kuma batutuwa da suka shafi harkokin sayen hannayen jari da yadda ya kamata su kasance a mahanga ta addinin musulunci. Ya ce ko shakka babu hakan zai taimaka wajen samun masani kamar yadda ya kamata dangane da harkokin kudi, kuma amfanin cibiyar ba zai takaitu da jami'ar ba kawai, har ma ga masu bukatar yin nazari kan hakan daga wasu kasashen musulmi za su iya amfana da wannan shiri.

411312

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: