IQNA

15:42 - July 15, 2009
Lambar Labari: 1802168
Bangaren siyasa da zamantakewa; Babban malamin addinin musulunci na kasar Labanan Allah Muhammad Hussain Fadlollah ya zargi Amurka da shiryawa musulunci zagon kasa a kowane lokaci.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga bangaren yada labarai na ofishinsa dake birnin Beirut na kasar Labanan cewa; Babban malamin addinin musulunci na kasar Labanan Allah Muhammad Hussain Fadlollah ya zargi Amurka da shiryawa musulunci zagon kasa a kowane lokaci. Allamah fadlollah ya zargi Amurka da shirya makarkashiya ga kasashen musulmi a tsawon tarihinta, kuma a wannan karon ma sabuwar gwamnatin Amurka ta zo wata sabuwar hanyar yaudarar musulmi, inda take kokarin nuna musu cewa tana son ta zauna lafiya da musulmi kuma ba tana kiyayya da addinin musulunci ba ne, ya ce yin hakan shi kansa babbar yaudara ce.

433055
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: