IQNA

15:42 - July 15, 2009
Lambar Labari: 1802505
Bangaren kasa da kasa; Wasu daga cikin mahardata kur'ani mai tsarki da adadinsu ya kai hamsin daga kasar Kuwait, sun kama hanya zuwa kasar Saudiyya da nufin kara fadada masaniyarsu kan kur'ani mai tsarki.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran Kuna cewa; Wasu daga cikin mahardata kur'ani mai tsarki da adadinsu ya kai hamsin daga kasar Kuwait, sun kama hanya zuwa kasar Saudiyya da nufin kara fadada masaniyarsu kan kur'ani mai tsarki, inda za su samu wani horo na musamman kan alkura'ni a wata cibiyar kula da harkokin kur'ani a birnin Makka. Bayanin ya ci gaba da cewa dukkanin wadanda za su samu horon dai mata ne, kuma an kasa su zuwa kashi daban-daban, akwai wadanda suke cikin rukuni na 'yan shekaru 15, haka nan kuma akwai wadanda suke cikin rukuni na 'yan shekaru sama da haka har zuwa shekaru ashirin da biyar. Wanda ke jagorantar tawagar mahardata kur'ani ya ce hakan zai taimaka musu matuka wajen mayar da hankali kan hardar ta su.

433807
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: