IQNA

Za A Gina Wata Cibiya Ta Kasa Da Kasa Domin Tattaunawa Tsakanin Addinai

22:46 - July 17, 2009
Lambar Labari: 1802689
Bangaren kasa da kasa; Mahalarta taron kasa da kasa da ake gudanarwa a birnin Viena na kasar Austria, sun cimma matsaya kan batun gina wata babbar cibiya ta kasa da kasa, da za ta kula da dukkanin batutuwa na tattaunawa tsakanin addinai.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na Alyaum cewa; Mahalarta taron kasa da kasa da ake gudanarwa a birnin Viena na kasar Austria, sun cimma matsaya kan batun gina wata babbar cibiya ta kasa da kasa, da za ta kula da dukkanin batutuwa na tattaunawa tsakanin addinai. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan tattaunawa tsakanin addinai dai an fara gudanar da ita ne tunkimanin shekaru biyu da suka gabata, bayan da sarkin kasar saudiyya Abdullah Bin abdulaziz ya bayar da shawara kan hakan. Haka nan kuma an gudanar da zama na biyu dangane da tattaunawa tsakanin addinai a birnin Madrid fadar mulkin kasar Spain, yanzu ana gudanar da shi a kasar Austria.

434375







captcha