A wannan hirar da aka watsa ta a jiya Juma’a shugaba Asad ya bayyana cewar goyon bayan da Turkiyya take ba wa ‘yan ta’adda, ko shakka babu zai sanya kasar cikin wani yanayi mai hatsarin gaske, don kuwa a cewar shugaba Asad ‘yan ta’addan tamkar kunama suke wacce a duk lokacin da ta ga ya dace za ta iya kai sara.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, tun daga lokacin barkewar rikicin kasar Siriya a watan Maris na 2011, gwamnatin kasar Turkiyya ta shiga sahun sansanin kasashen larabawa da na yammaci wajen kulla makarkashiya kan kasar Siriyan. Tun daga wancan lokacin ne dai gwamnatin Turkiyyan ta bude kan iyakokinta ga ‘yan ta’addan da share musu fagen shigowa kasar Siriyan, baya ga kafa wasu sansanoni a cikin kasar don horar da ‘yan ta’addan.
Wannan dai ba shi ne karon farko da shugaban na Siriya da sauran jami’an kasar da ma masana suke jan kunnen gwamnatin Erdogan din kan irin wannan goyon baya da take ba wa ‘yan ta’adda a kasar Siriyan da ma wasu kasashen da suke makwabtaka da ita ba, bisa la’akari da abubuwan da suka faru a baya kan yadda irin wadannan kungiyoyi suka koma kan iyayengijinsu na su a duk lokacin da suka kai ga abin da suke so ko kuma suka gagara cimma hakan.
Masana suna ganin wannan jan kunnen na shugaba Asad wani lamari ne da ya yi daidai da hankali, saboda irin masaniyar da yake da ita na irin yadda gwamnatin Turkiyyan take ba da horo ga ‘yan ta’addan da ake turo su kasarsa da nufin kifar da gwamnatin kasar.
Ko shakka babu manufar wannan sansani na kasashen larabawa da na yammaci wajen goyon bayan ‘yan ta’addan ita ce kifar da gwamnatin kasar Siriyan saboda irin siyasarta ta tsayin daka da kuma tinkarar ‘yan mulkin mallaka na duniya.
Kasar Siriya a koda yaushe ta kasance mai nuna goyon bayan al’ummar Palastinu da ake zalunta. Don haka ne da dama suke ganin wannan yaki da aka kaddamar kan kasar Siriya, an kaddamar da shi ne sakamakon irin goyon bayan da take ba wa kungiyoyin gwagwarmaya a kasar Labanon da Palastinu. To sai dai kuma har ya zuwa yanzu, bayan kimanin shekaru uku na irin wannan goyon baya na kudade da makamai da bayanan sirri da wadannan gwamnatoci musamman na Saudiyya da Qatar da Turkiyya suke ba wa ‘yan ta’addan, wadanann kasashe sun gagara cimma wannan manufa da suka shata, bil hasali ma a koda yaushe dakarun gwamnatin Siriya sai dada kwato yankunan da ‘yan ta’addan suka kame.
A bangare guda kuma dukkanin kokarin da wadannan kasashen suka yi wajen ganin sun sanya Amurka da kawayenta na kasashen Turai sun kai wa Siriyan harin soji, abin ya ci tura sakamakon tsayin dakan gwamnatin Siriya da kawayenta na yankin nan. Dukkanin wadannan batutuwan suna daga cikin abubuwan da a halin yanzu suke ci wa Turkiyya da kawayenta tuwo a kwarya, a bangare guda kuma ‘yan ta’addan da aka shigo da su kasar sun fara tunanin mece ce makomarsu bayan shan kashin da suke yi da kuma kokarin juya musu baya da kasashen yammacin suke yi.
Wannan sabon yanayin dai shi ne abin da ya fara sanya damuwa cikin zukatan jami’an gwamnatin Turkiyyan da ya sanya shugaban kasar Abdullah Gol a kwanakin baya fitowa da fadin cewa kasar Turkiyya tana fuskantar barazana daga ‘yan ta’addan da suke shigowa kasar daga Siriya.
1302345