IQNA

An Fara Gudanar Da Gasar Kur'ani Ta Kasa Da Kasa A Libya

16:36 - September 15, 2009
Lambar Labari: 1826651
Bangaren kasa da kasa; An fara gudanar da gasar karatun kur'ani mai tsarki ta kasa da kasa a birnin Tripoli na kasar Libya, wanda kuma wannan shi ne karo na biyar da ake gudanar da irin wannan gasa a kasar.
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin internet na arabonline cewa; An fara gudanar da gasar karatun kur'ani mai tsarki ta kasa da kasa a birnin Tripoli na kasar Libya, wanda kuma wannan shi ne karo na biyar da ake gudanar da irin wannan gasa a kasar. Bayanin ya ci gaba da cewa gasar tana samun halartar makaranta da kuma mahardata kur'ani mai tsarki daga kasashen musulmi daban-daban. Diyar shugaban kasar kasar Libya Aisha ita ce ke jagorantar gudanar da tarukan gasar a binin Tripoli. 464643captcha