Bangaren kasa da kasa; Za a watsa gasa kasa da aksa ta tilawa da tawidi na kur'ani mai girma na kananan yara daga shekaru takwas zuwa sha uku daga kasashen Katar ,Marokko,Tunisiya.Masar,Suriya da Aljeriya kuma a watan Ramadan ne za a watsa wannan gasar ta Aljazira ta kananan yara.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ikna bayan ta nakalto daga jaridar Masar ta Alyaum Alsabi'I ta watsa rahoton cewa; Za a watsa gasa kasa da aksa ta tilawa da tawidi na kur'ani mai girma na kananan yara daga shekaru takwas zuwa sha uku daga kasashen Katar ,Marokko,Tunisiya.Masar,Suriya da Aljeriya kuma a watan Ramadan ne za a watsa wannan gasar ta Aljazira ta kananan yara. A ranar ashirin da bakwai ga watan Ramadana ne za fara gasar tare da sauraren karatun karamin yaro da yafi kankanta daga cikin yan takara.
595449