IQNA

An Kawo Karshen Gasar Hardar Kur'ani Ta Muaz A Fadin Yaman

12:05 - July 21, 2010
Lambar Labari: 1959842
Bangaren kasa da kasa: an kawo karsehn gasar harda da karatun kur'ani mai girma ta Mu'az karo na goma sha daya da ake gudanarwa a fadin kasar Yaman kuma a ranar ashirin da tagwas na watan Tir na shekarar hijira shamsiya aka kawo karshenta tare da bayyana sunayen wadanda suka lashe gasar a garin Tauz na Yaman.

Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna bayan ta nakalto daga majiyar labarai ta gwamnatin kasar ta yaman Saba'anet ta watsa rahoton cewa; an kawo karsehn gasar harda da karatun kur'ani mai girma ta Mu'az karo na goma sha daya da ake gudanarwa a fadin kasar Yaman kuma a ranar ashirin da tagwas na watan Tir na shekarar hijira shamsiya aka kawo karshenta tare da bayyana sunayen wadanda suka lashe gasar a garin Tauz na Yaman.Gudanar da irin wannan gasar karatun kur'ani zai karawa matasa karfin guiwa da hamzartar da su wajen rungumar karatun Kur'ani mai girma.



617977
captcha