IQNA

Taro Kan Matsayin Kur'ani A Rayuwar Musulmi A Kasar Turkiya

16:07 - August 03, 2010
Lambar Labari: 1966616
Bangaren kasa da kasa; Za a gudanar da wani zaman taro wanda zai yi dubi kan matsayin kur'ani mai tsarki a cikin rayuwar musulmi ta yau da kullum, wanda bababr cibiyar fatawa ta birnin Siirt na kasar za ta shirya gudanarwa.
Kmafanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakalto dikkarhabar a shafinsa na yanar gizo cewa, za a gudanar da wani zaman taro wanda zai yi dubi kan matsayin kur'ani mai tsarki a cikin rayuwar musulmi ta yau da kullum, wanda bababr cibiyar fatawa ta birnin Siirt na kasar za ta shirya gudanarwa a nan gaba.

Bayanin ya ci gaba da cewa wannan zaman taro zai mayar da hanakali ne kan koyarwar kur'ani da matsayin rayuwar musulmi, gami da koyar da dan adam muhimman abubuwan day a kamata koya daga kur'ani.

A lokacin gudanar da zaman taron za a gabatar da laccoci, da kuma raba makaloli da malaman jami'oi muuslmi suka gami da manazarta suka rubuta kan hakan.

625238
captcha