Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna bayan ta nakalto daga majiyar labarai ta muhit ta watsa rahoton cewa; wasu daga cikin malaman jami'ar Azhar a kasar masar ta yi kaukausar sukar matakin da wata coci a jahar Florida a Amerika ta dauka na ware rana ta musamman a duniya ta kona Kur'ani da cewa wani sabon makirci ne na coci-coci a yammacin Turai kan Musulunci da musulmi.
Wannan makirci ba zai iya samin karbuwa da cimma burin makirci da coci-coci ke son aiwatarwa a kan musulmi da Musulunci domin kuwa a yau makirci komin kashinsa kan musulmi da Musulunci a duniyya.
625845