Kamfanin dillancin labarai na cibiyar Ikna mai kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran bayan ya nakalto daga jaridar Khalij Taiz ya watsa rahoton cewa;
komitin shirya gasar karatun kur'ani ta kasa da kasa a birnin Dubai na hadeddiyar daular larabawa ya bayyana sunayen alkalai da za su jagoranci wannan gasar. Ibrahim Bumlaha shugaban komitin shirya wannan gasar ya bayyana cewa; sa'ud bin Abdul Aziz Ganim daga Saudiya,Salih Ahmad Shimi daga kasar Masar,Balal Yahya Barudi daga kasar Labanon,Ahmad Samih Usmana daga kasar Jodan,Hasan Ahmad Abu Nasr daga Amerika sune za su jagoranci gasar karatun kur'ani ta kasa da kasa a birnin Dubai.
627469