Bangaren kasa da kasa; a daidai wannan lokaci na kuratowar watan azumin ramadana an rarraba kur'anai da aka tarjama da harsunan faransanci da Spaniyanci da kuma yaren Amazigi na kabilar barbar ta arewacin Afrika a tsakanin masallata a masallatai da cibiyoyin koyar da kur'ani da kumgiyoyin bada agaji da ci gaban al'adu a Aljeriya suka yi.
Bayan ta nakalto daga majiyar labarai ta Mahit .kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ya watsa rahoton cewa; a daidai wannan lokaci na kuratowar watan azumin ramadana an rarraba kur'anai da aka tarjama da harsunan faransanci da Spaniyanci da kuma yaren Amazigi na kabilar barbar ta arewacin Afrika a tsakanin masallata a masallatai da cibiyoyin koyar da kur'ani da kumgiyoyin bada agaji da ci gaban al'adu a Aljeriya suka yi.Wannan mataki ne da zai karawa musulmi karfin guiwar fuskantar wannan wata na azumi mai tsarki da rahama.
627909