Bangaren kasa da kasa; a bayyana tsari da shirye-shiryen da aka tsara za a gudanar ta fuskar al'adu a gasar kasa da kasa ta karatun kur'ani a birnin Dubaai na hadeddiyar daular larabawa kuma an bayana hakan ne a ranar juma'a da ta gabata sha biyar ga watan Murdad na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya da masu kula da shirya wannan gasar suka yi.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci tai ran bayan ta nakalto daga jaridar Khaleej Times ta watsa rahoton cewa; a bayyana tsari da shirye-shiryen da aka tsara za a gudanar ta fuskar al'adu a gasar kasa da kasa ta karatun kur'ani a birnin Dubaai na hadeddiyar daular larabawa kuma an bayana hakan ne a ranar juma'a da ta gabata sha biyar ga watan Murdad na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya da masu kula da shirya wannan gasar suka yi.Ibrahim Bumalha shugaban komitin shirya wannan gasar ya bayyana cewa; a dabra da gasar kasa da kasa ta karatun kur'ani mai girma ta kasa da kasa za a gudanar da jawabai da lakcoci guda ashirin da takwas da suka shafi kur'ani da kuma wasu jawabai ashirin da biyar da harshen larabci da kuma wasu biyu da yaren Malawi da kuma daya da yaren Bangali.
627759