Kamfanin dillancin Labarai na ikna bayan ya nakalto daga jaridar Hadeddiyar daular Larabawa ta watsa rahoton cewa; Tawagar Ahlul Baiti Ta Duniya ce ta shiraya wannan shiri tare da hadin guiwar ofishin kula da harkokin Musulunci da bada agaji na birnin Dubai a Hadeddiyar Daular Larabawa kuma wannan shiri na musamman a watan azumi na tafsirin Kur'ani ga mata musulmi tsuraru yan kasashen waje mazauna wannan kasa.
Umar Muhammad Alkhatib mukaddashin babban sakataren kungiyar Alittihad ya kara da cewa;burin wannann shiri shi ne bawa musulmi mata mazauna birnin na dubai damar samun alfanon da ke tattare da wannan wata mai albarka da kuma anfanuwa da shi.
636287