IQNA

An baje Kolin Tarjamar Sahifa Sajjadiya Da Yaren Urdo A Baje Kolin Kur'ani Na Kasa Da Kasa

12:10 - August 19, 2010
Lambar Labari: 1976803
Bangaren kasa da kasa; a kasuwar baje kolin kur'ani ta kasa da kasa a birnin Tehran an baje kolin tarjamar Sahifa Sajjadiya da harshen Urdo a dakin Hai'atul Ansarul Mustapha (SWA).

Kamfanin dillancin labarai na Ikna day a ziyarci gurin da ake gudanar da wannan kasuwar baje kolin ya watsa rahoton cewa; a kasuwar baje kolin kur'ani ta kasa da kasa a birnin Tehran an baje kolin tarjamar Sahifa Sajjadiya da harshen Urdo a dakin Hai'atul Ansarul Mustapha (SWA).Wannan kasuwar baje kolin it ace irinta karo na sha takwas da ake gudanarwa kan kur'ani mai girma a babban filin salla na imam Khomeini ® wannan daki an warewa jami'ar Almustapha (SWA) al'alami da bayan wannan tarjama Ta Sahifa sajjadiya ta kuma kawo tarjamomin da dama da suka hada da tarjamar Mafatihul Janan a cikin harshen turanci guda biyu da kuma Fahrasin kur'ani mai girma da yaren turanci da kuma tarjumar kur'ani mai girma tare da tafsirin Said Kutub da yaren Bangali guda uku.



636433
captcha