IQNA

An Gudanar Da Zama Da Ya Kebanci Iyalai A Baje Kolin Kur'ani

15:36 - August 26, 2010
Lambar Labari: 1981752
Bangaren kur'ani; An gudanar da wani zama na musamman da ya kebanci iyalai a baje kolin kur'ani mai tsarki na duniya da ake gudanarwa abirnin Tehran, wanda a ka gudanar a babban dakin taruka na Mofatteh.


Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, an gudanar da wani zama na musamman da ya kebanci iyalai a baje kolin kur'ani mai tsarki na duniya da ake gudanarwa abirnin Tehran, wanda a ka gudanar a babban dakin taruka na Mofatteh da ke wurin da ake gudanar da tarukan baje kolin.

Bayanin ya ci gaba da cewa bangaren lardin Razavi ne ya shirya gudanar da wannan zama, da nufin wayar da kan iyalai dangane matsayinsu a mahangar kur'ani, da kuma yadda ya shimfida hanyoyi na rayuwa ta iyalai, da hakan zai bayar da kyakkyawan misali a cikin rayuwar al'umma.

An gudanar da jawabai da dama, wadanda suka danganci matsayin iayalai da kuma rawar da suke takawa a cikin rayuwa ta zamantakewa, daga cikin wadanda suka gabatar da jawabai har da Hojjatol Eslam Gevahi.

640816





captcha