IQNA

Wakilin Jagoran Yan shi'a A Pakistan Sun gana Da Shugaban Jihadul Daneshga Qum

14:18 - August 30, 2010
Lambar Labari: 1984442
Bangaren siyasa da zamantakewa; wakilin jagoran yan shi'a a kasar Pakistan Allama Said Sajid Nakawi a ranar bakwai ga watan Sharivar ne ya gana da Muhammad Ibrahim Fakih Zade shugaban kungiyar Jihadi a Jami'ar birnin Qum ibda ya mika masa bukatar a taimakawa wadanda ambaliyar ruwa ta yi masu banna.

Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran daga reshensa da ke birnin Qum ya watsa rahoton cewa; wakilin jagoran yan shi'a a kasar Pakistan Allama Said Sajid Nakawi a ranar bakwai ga watan Sharivar ne ya gana da Muhammad Ibrahim Fakih Zade shugaban kungiyar Jihadi a Jami'ar birnin Qum ibda ya mika masa bukatar a taimakawa wadanda ambaliyar ruwa ta yi masu banna. Wannan ambaliyar ruwa da ta abku a kasar ta Pakistan a cikin shekaru arba'in da suka gabata ba a ga irinta ba kuma ta hadda banna da asara ta raid a ta dukiya ga mutane sama da miliyan ashirin da biyu. Har ila yau mutanan da lamarin ya shafa suna bukatar agaji cikin gaggauawa.


644014
captcha