IQNA

Taro Kan Safkar Kur'ani A Jami'ar Musulunci Ta Burnai

14:23 - September 06, 2010
Lambar Labari: 1988726
Bangaren kasa da kasa; An Gudanar da wani zaman taro kan safkar wahayin kur'ani mai tsarki a jami'ar Musulunci da ke tsibirin Burnai a daidai lokacin da ake cikin watan Ramadan mai alfarma.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, an Gudanar da wani zaman taro kan safkar wahayin kur'ani mai tsarki a jami'ar Musulunci da ke tsibirin Burnai a daidai lokacin da ake cikin watan Ramadan mai alfarma kamar yadda aka gudanar a wasu kasashen.

Bayanin ya ce wanna taro ya samu halartar masana daga sassa daban-daban na kasar, inda malamai suka gabatar da laccoci dangane da matsayin kur'ani mai tsarki, da kuma muhimmancin girmama ranar safkar wahayi.

Daga cikin wadanda suka halarci taron hard a shugabannin jami'ar da kuma daruruwan dalibai, musamman ma masu gudanar da nazari a bangaren ilmomin kur'ani.

648446



captcha