IQNA

Jerin Gwanon Malaman jami'oin Qom Kan Kone Kur'ani

16:29 - September 16, 2010
Lambar Labari: 1995225
Bangaren kur'ani; Dubban malamai da daliban jami'in birnin Qom ne suka gudanar da zanga-zangar yin Allawadai da kone kur'ani mai tsarki da wasu tsirarun kiristoci suka yi a kasar Amurka da nufin muzgunawa al'ummar musulmi.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga bangaren yada labaransa na birnin Qom da ke cikin jamhuriyar Musulunci ta Iran an bayyana cewa, dubban malamai da daliban jami'in birnin Qom ne suka gudanar da zanga-zangar yin Allawadai da kone kur'ani mai tsarki da wasu tsirarun kiristoci suka yi a kasar Amurka.

Dubban masu zanga-zangar sun yi tar era taken yin Allawadai da matakin da nuna ko in kula da wasu daga cikin gwamnatocin kasashen musulmi suka dauka kan wannan lamari, tare da la'antar Amurka da kuma dukkanin masu hannu wajen kone littafin Allah mai tsarki.

Yanzu haka dai da dama daga cikin musulmi a kasashen duniya na ci gaba da nuna fushinsu kan wannan mummnan aiki na cin zarafin musulmi day a wakana akasar Amurka.

655087



captcha