IQNA

Musulmin Georgia Sun Nuna Fushinsu Kan Wulakanta Kur'ani

12:11 - September 19, 2010
Lambar Labari: 1996761
Bangaren siyasa da zamantakewa; Musulmin kasar Georgia sun gudanar da wani gangami a birnin Marintoli na kasar, domin nuna fushinsu kan cin zarafin addinin Musulunci da aka yi ta hanyar kone kur'ani mai tsarki.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga bangaren hulda da jama'a na ma'aikatar kula da harkokin al'adu cewa, musulmin kasar Georgia sun gudanar da wani gangami a birnin Marintoli na kasar, domin nuna fushinsu kan cin zarafin addinin Musulunci da aka yi ta hanyar kone kur'ani mai tsarki a kasar Amurka.

Taron gangamin ya hada mabiya mazhabar shi'a da 'yan sunna inda aka yi ta rera taken yin Allawadai da wannan mummunan aiki na kone kur'ani, tare da kiran sauran musulmin duniya da su mike domin bayar da kariya ga addininsu.

Tun bayan da wani mai kiran kansa malamin addinin kirista a Amurka ya kirayi masu irin tunaninsa da su sanya rana 11 ga watan satum ta zama ranar kone kur'ani, yak e ci gaba da fuskantar martanin musulmi.

656990



captcha