IQNA

Taro Mai Taken Ahlul-Bait A Kur'ani Da Sunna A Turkiya

11:27 - September 26, 2010
Lambar Labari: 2001469
Bangaren kasa da kasa; Za a gudanar da wani zaman taro a kasar Turkiya da zai yi nazari dangane da matsayin iyalan gidan manzon Allah (SAW) a cikin kur'ani mai tsarki da kuma sunnar ma'aiki.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da samu daga shafin yanar gizo na miras maktub an bayyana cewa, za a gudanar da wani zaman taro a kasar Turkiya da zai yi nazari dangane da matsayin iyalan gidan manzon Allah (SAW) a cikin kur'ani mai tsarki da kuma sunnar ma'aiki tsira da aminci su tababta a gare shi.

Bayanin ya ce wannan zaman taro na tattare da muhimamn batutuwa da suka sanya musulmi gudanar da bincike kan matsayin iyalan gidan manzon Allah (SAW) a cikin lokutannan.

Matsayin iyalan gidan manzon Allah (SAW) a cikin addinin musulunci gishiki ne da addinin Musulunci ya doru kansa, ta yadda barin su daidai yake da barin addini na asali.

661862


captcha