Bangaren kur'ani, Reshen cibiyar raya al'adu da ilimin muslunci ta Iran dake birnin Baku na kasar Azarbaijan ya mayar da martani ga masu keta alfarmar kur'ani mai tsarki, ta hanyar yin rubuce-rubuce a cikin jaridun kasar.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, reshen cibiyar raya al'adu da ilimin muslunci ta Iran dake birnin Baku na kasar Azarbaijan ya mayar da martani ga masu keta alfarmar kur'ani mai tsarki, ta hanyar yin rubuce-rubuce a cikin jaridun kasar da suka fito a wannan mako.
Kasar Azarbaijan dai na daya daga cikin kasashen musulmi da suke da mabiya mazhabar shi'a da dama, inda su ne suke da rinjaye, al'ummar kasar dai ta nuna rashin amincewarta da keta alfarmar kur'ani mai tsarki da aka yi a kasar Amurka.
Yanzu haka dai bayanan da cibiyar kula da harkokin ilmi da bunkasa al'au ta Iran ta dauki nauyin bugawa a jaridun kasar ya yi tasiri matuka wajen wayar da kan mutane halin da ake ciki.
664843